Atiku Ba Labari, Kotu Ta Bashi Rashin Nasara

0 180

A yau ne Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Shugaban Ƙasa ta yi watsi da ƙarar da Atiku Abubakar, ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar PDP da jam’iyyar suka shigar, inda suke buƙatar Kotun ta soke nasarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya samu a zaɓen Shugaban Ƙasa na 2019.

Kotun, a wani hukunci da gaba ɗaya alƙalan suka amince da shi, ta yanke hukuncin cewa Atiku da PDP sun kasa kawo hujjojin da suke so a soke nasarar Shugaba Buhari da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: