A Najeriya, Jihar Kogi ce kaɗai ba ta fara amfani da allurar rigakafin korona ba daga cikin jiha 36 da ke ƙasar ya zuwa ranar Lahadi.

An yi wa ‘yan Najeriya 513,626 rigakafin a sauran jihohi ya zuwa Lahadi, a cewar alƙaluman da hukumar lafiya a matakin farko National Primary Health Care Development Agency (NPHCDA) ta fitar.

Bisa alƙaluman da hukumar ta wallafa, Kogi ce kaɗai ba ta yi wa ko mutum ɗaya ba yayin da Kebbi da Taraba suka yi wa mutum ɗai-ɗai kowaccensu.

Kwanakin baya, Gwamnan Kogi Yahaya Bello ya yi kira ga ‘yan Najeriya da kar su bari a yi musu allurar, yana mai zargin cewa ba ta da inganci.

Jihar Legas ce kan gaba a yawan waɗanda aka yi wa, inda ta yi wa mutum 110,042. Ita ce kuma ke da mafi yawan waɗanda ke kamuwa da cutar a Najeriya.

Jihar Ogun ce ke biye mata da mutum 47,507, sai Kaduna mai 38,063 da kuma Bauchi mai mutum 32,482.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: