Kungiyar SERAP ta maka kamfanin man fetur na kasa NNPCL a kotu

0 330

Kungiyar SERAP mai fafutukar Kare Hakkokin Tattalin Arziki da tabbatar da demokradiyya ta maka kamfanin man fetur na kasa NNPCL a gaban sharia, kan rashin bayyana cikakkun alkaluman yadda ake hako mai da safarar sa a kullum da kuma yawan kudaden shiga da ake samu daga man fetur tun bayan cire tallafin man fetur a watan Mayun shakerar nan.

A kwanakin baya ne dai tsohon gwamnan babban bankin kasa (CBN), Sunusi Lamido Sanusi ya yi zargin cewa kamfanin na NNPCL ya gaza samar da isassun kudaden kasar waje a cikin baitul malin kasarnan duk da cire tallafin man fetur.

Kungiyar  ta SERAP dai na neman kotu ta ba da umarni tare da tilastawa kamfanin na NNPCL da ya bayyana cikakkun bayanai kan gangunan man da Najeriya ke hakowa da kuma wadanda take fitar da su a kullum da kuma yawan kudaden shigar da ake samu tun bayan cire tallafin man fetur.

SERAP tana kuma neman kotu ta tilastawa kamfanin na NNPCL ya bayyana cikakkun bayanai na biyan Naira Tiriliyan 11 da aka biya a matsayin tallafi man fetur daga 1999 zuwa Mayu 2023, gami dayin cikakken bayanin yadda aka salwantar da kudaden. Sai dai kawo yanzu ba a kayyade ranar da za a saurari karar ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: