Wasu mahara dauke da makamai sun kashe fararen hula biyar

0 344

Yan sanda a Kenya sun ce wasu mahara dauke da makamai sun kashe fararen hula biyar da suka kai hari a wasu kauyuka biyu a kudu maso gabashin Kasar.

Majiyar ‘yan sandan tace an kai harin a jiya a kauyukan Juhudi da Salama da ke gundumar Lamu mai iyaka da kasar Somaliya.

Maharan sun kuma kona gidaje tare da lalata dukiyoyi.

An daure wani dattijo mai shekaru 60 da igiya kuma an tsaga makogwaronsa, tare da kone gidansa.

An kashe wasu uku a makamancin haka yayin da aka harbe na biyar.

Wani dalibin makarantar sakandare na daga cikin mutane biyar da aka kashe. Wani mazaunin yankin mai suna Ismail Hussein ya ce mayakan sun yi awon gaba da kayan abinci kafin su tafi, inda suka yi ta harbin iska.

Leave a Reply

%d bloggers like this: