Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, Farfesa Attahiru Jega da tsohon limamin katolika na Abuja, Cardinal John Onaiyekan, sun gayawa shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa yan Najeriya na fuskantar manyan wahalhalu biyu na rashin tsaro da illar annobar corona.

A saboda haka suka yi kira ga shugaban kasa da yayi duk mai yiwuwa wajen magance rashin tsaro, ko da kuwa sai ya tsige shugabannin hukumomin tsaro.

Sun sanar da haka cikin wata sanarwa dauke da sa hannun ‘ya’yan wata kungiya mai fafutukar zaman lafiya da mulki nagari.

Sun nemi shugaban kasa da ya assasa shirin tattaunawa domin magance tashe-tashen hankula daban-daban, wadanda suka hada da na kabilanci da addini.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: