Shugaban majalissar Dattawa ta kasa Femi Gbajabiamila, yace Gwamnan Jihar Lagas Babajide Sanwo-Olu yace jihar tana bukatar Naira Tiriliyan Daya domin a sake gina wajen da masu zanga-zangar #EndSARs suka  rushe.

Gbajabiamila ya fadi haka a lokacin da yake hira da yan jaridu a majalissar bayan ziyarar gani da ido kan wuraren da masu zanga zangar suka barnatar a birnin Lagas.

Ya ce majalissar zatayi duk mai yuwuwa domin biyan diyya ga wadanda rikicin ya rutsa da su, da suka hadar da jami’an yan sanda da suka rasa rayukansu.

Ya kuma bukaci matasa da kwantar da hankulansu, domin dawo da zaman lafiya, tare da bayyana kwarin gwiwarsa kan hadin kan kasa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: