An raba masara buhu 260 ga wadanda ambaliya ta yiwa ɓarna a Birnin-Kudu

0 210

Hukumar bada agajin gaggawa ta Jihar Jigawa ta bada gudunmawar buhunan masara 260 ga wadanda suka gamu da ambaliyar ruwa a garuruwan Shungurum da Gangara da Babaldu da Argun da Malamawa da kuma Kuja dake yankin Karamar Hukumar Birnin-Kudu.

Sakataren zartarwar hukumar, Yusuf Sani Babura, ya sanar da haka lokacin rabon kayan a garin Babaldu.

Da yake jawabi, Yusuf Sani Babura yace bugu da kari, hukumar ta bada tallafin buhunan garin kwaki 50 da na sikari 7 ga wadanda iftila’in ya shafa. Sani Babura ya ce an bayar da tallafin ne domin rage musu radadin rayuwa da suke fuskanta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: