Helkwatar tsaro tace sojin sama na opearation Hadarin Daji sun lalata karin wani sansanin barayi tare da kashe batagari da dama a dajin Kwayanbana a jihar Zamfara.
Jagoran yada labaran ayyukan tsaro, John Enenche, cikin wata sanarwa da ya fitar yau a Abuja yace anyi luguden wuta ranar 7 ga watan Yunin da muke ciki, a cigaba da yakin sama da ake gudanarwa karkashin shirin operation accord.
- IFFHS Ta Saɓa da FIFA, Ta Ayyana Lionel Messi A Matsayin Gwarzon Ɗan Wasan Gasar Kofin Duniya
- Casemiro Ya Koma Inter Miami Kyauta Bayan Karewar Kwantiraginsa
- Hisbah Ta Gargadi Masu Neman Shiga Shirin Auren Gata Kan Masu Damfara
- Trump Ya Aike Wa Tinubu Wasiƙa, Ya Yaba da Ƙwazon Gwamnatinsa Wajen Yaƙi da Ta’addanci
- Gwamnatin Sokoto Ta Bai Wa Sojojin Najeriya Gudummuwar Motocin Sulke 62
Majon Janar Enenche yace an samu nasarar bayan wani rahoton sirri, leken asiri da sa’ido ya tabbatar da cewa an boye wasu tantuna a karkashin duhun bishiyoyin dajin.
Yace rahoton sirrin ya kuma bayyana cewa ana amfani da
kogo da ake samu a wajen a matsayin maboyar barayin tare da sanannen jagoransu,
Dogo Gede.