Home Labarai Archive by category Ilimi

Ilimi

Ilimi Labarai

Cibiyar horas da malaman makaranta ta ƙasa (NTI) tana aikin horas da malaman makaranta 925

Cibiyar horas da malaman makaranta ta kasa (NTI) da ke Kaduna tana aikin horas da malaman makaranta 925 akan fannoni masu muhimmanci a taron karawa juna sani na malamai a karkashin shirin dorewar manufofin cigaba. Ana gudanar da aikin bayar da horon a fadin jihoshi 36 da babban birnin tarayya. Continue reading
Ilimi Labarai

Hukumar jami’ar Bayero dake Kano ta amince da karawa malaman makarantar da ma’aikatanta da basa koyarwa matsayi su 772

Hukumar jami’ar Bayero dake Kano ta amince da karawa malaman makarantar da ma’aikatanta da basa koyarwa matsayi su 772. Jami’ar ta bayyana hakan ne ta bakin Sakataren yada labarai na jami’ar Mr. Lamara Garba, wanda ya fitar da sanarwar ga manema labarai a birnin Kano. Sanarwar tace, andaga likafar wasu malamai 7 wadanda yanzu haka […]Continue reading
Ilimi

An kammala domin fara karatu a shekarar karatu ta 2021 zuwa 2022 a jami’ar Khadija dake Majia

Shugabar jami’a mai zaman kanta ta Khadija da ke garin Majia a karamar hukumar Taura ta jihar nan, Farfesa Hassana Sani Darma, ta bayyana cewa shirye-shirye sun kammala domin fara karatu a shekarar karatu ta 2021 zuwa 2022. Shugabar jami’ar ta sanar da haka yayin ganawa da manema labarai, bayan ziyarar gani da ido da […]Continue reading
Ilimi Labarai

Gwamnatin jihar Jigawa ta bukaci masu yin NYSC da su zauna a jihar

Jagorar hukumar matasa masu yiwa kasa hidima (NYSC) a jihar Jigawa, Hajiya Aishatu Adamu, ta shawarci masu yiwa kasa hidima da aka turo jiharnan su zauna a jihar. Aishatu Adamu ta ba da shawarar yau a jawabin maraba da ta yi wajen kaddamar da bikin wasanni da al’adu na bana a Dutse. Ta yi bayanin […]Continue reading
Ilimi Labarai

Kwamishinan ilimi Kimiyya da fasaha na jihar Jigawa ya kaddamar da kwamitin da zasu ziyarci manyan makarantun gaba da sikandire

Kwamishinan ilimi Kimiyya da fasaha na jihar Jigawa, Dakta Lawan Yunusa Danzomo ya kaddamar da wakilan kwamitin da zasu ziyarci manyan makarantun gaba da sikandire na jihar nan domin ganin halin da suke ciki tare da gabatarwa da gwamnati rohoto. A jawabinsa lokacin bikin kaddamarwar kwamishinan ya ce makasudin kafa kwamatin shi ne shigar da […]Continue reading
Ilimi Labarai

Gwamnatin jihar Jigawa ta fara gabatar da sabbin shirye-shiryen koyan karatu ta hanyar rediyo

Gwamnatin Jihar Jigawa ta fara gabatar da sabbin shirye-shiryen ga magidanta maza da mata domin koyan karatu ta hanyar radio. A jawabinsa Sakataren zartarwa na hukumar Ilimin Manya na Jihar Jigawa Dr Abbas Abubakar Abbas ya ce magidanta dubu 1,000 ne zasu sami akwatinan radion domin koyan karatu ta hanyar radio. Dr Abbas A Abbas […]Continue reading
Ilimi

Mutum 1466 ne ake tantancewa a shirin gwamnatin tarayya na Npower a karamar hukumar Hadejia

A kalla Matasa Maza da Mata dubu 1,466 ne ake saran tantancewa bayan sun samu Damar shiga Shirin gwamnatin tarayya na Npower a nan karamar hukumar Hadejia. Shugaban Kula da Shirin Tallafi na Karamar Hukumar Hadejia Alhaji Isah Idris Abubakar, shine ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban Karamar hukumar wanda ya […]Continue reading
Ilimi Jigawa Labarai

Senator Sabo Nakudu ya bada gudummawar kwamfutoci ga dalibai biyar-biyar na kananan hukumomin 7

Dan majalisar Dattawa mai wakiltar Jigawa ta tsakiya, Senator Sabo Muhammad Nakudu, ya bada gudummawar kwamfutoci ga dalibai 35 ga dalibai biyar-biyar na kananan hukumomin 7 da yake wakilta wadanda suke karatu a manyan makarantu daban-daban. Da yake mika kwamfutocin ga daliban a ofishin Kungiyar ci gaban masarautar Dutse, Senator Sabo Nakudu ya ce ya […]Continue reading
Ilimi Labarai Security

UNICEF: Akwai yiwuwar yara miliyan daya a Najeriya su daina zuwa makaranta saboda barazanar sace su

Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce akwai yiwuwar yara miliyan daya a Najeriya su daina zuwa makaranta saboda barazanar da suke fuskanta ta sace daliban makarantu da aka yi a kasar a wannan shekara. A ranar Laraba Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wannan sanarwa inda ta ce, ‘yan bindiga sun […]Continue reading
Ilimi Labarai

An bayyana Arewa a matsayin wuraren da aka fi samun masu satar jarabawa

An bayyana Jihohin Bauchi, Borno, Kano, da kuma Kebbi a matsayin wuraren da aka fi samun masu satar Jarabawa a kasar nan. Shugaban Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Sikandire ta NECO Farfesa Dantani Wushishi, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da mukala mai taken Illolin satar Jarabawa. Mista Wushishi ya ce shekaru 5 […]Continue reading